Premier League: Man United ta casa Newcastle a Old Trafford

Anthony Martial

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sau hudu kenan Martial yana ci wa United kwallo sama da daya a wasa guda a Premier

Anthony Martial ya zira kwallo biyu a wasan da Manchester United ta casa Newcastle United da ci 4-1 a filin wasa na Old Trafford.

Martial ya fara da farke kwallon da matashin dan wasa Matty Longstaff ya ci wa Newcastle kafin wani matashin Mason Greenwood ya ci wa Man United kwallo ta biyu.

Marcus Rashford ya ci ta uku da ka bayan da Wan-Bissaka ya bugo masa ita a sama daga bangren dama - kwallonsa ta 11 kenan a Premier ta bana.

Martial ya kara ta hudun kuma saura kiris ya zama dan wasan Man United na farko da ya ci uku rigis tun shekarar 2013, amma sai kwallon ta daki tirke.

Yanzu Man United tana mataki na bakwai da maki hudu tsakaninta da 'yan hudun saman teburi.

Ranar ta Martial ce

Asalin hoton, Getty Images

Kwallon Martial ta biyu, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, ita ce karo na hudu da dan kasar Faransar yake ci wa Man United kwallo sama da sau daya a wasa daya tun sanda ya fara yi wa United wasa a 2015.

Babu mamaki mataimakin mamallakin kulob din wato Ed Woodward zai yi murnar cewa ya yi daidai da ya hana Jose Mourinho sayar da dan wasan a farkon kakar da ta gabata.

Har yanzu magoya baya suna sonsa domin kuwa ya sha tabi a lokacin da yake fita daga fili bayan Juan Mata ya karbe shi.