Premier League: Ancelotti ya fara da nasara a Everton

Carlo Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images

Carlo Ancelotti ya fara wasa da kafar dama a wasan farko da ya jagoranci Everton sakamakon doke Burnley da kungiyarsa ta yi a filin wasa na Goodison Park.

Dan kasar Italiyan mai shekara 60 wanda kuma ya lashe kofin Premier da FA a Chelsea a 2009, ya karbi Everton a makon da ya gabata kuma ya samu maraba daga magoya baya.

Burnley wadda ta ci wasan Premier biyu a jere, ta kusa jefa kwallo tun a minti na 3 da fara wasa, da kyar Yerry Mina ya yakice ta a kan layin raga.

Mai tsaron ragar Burnley ya yi matukar kokari lokacin da ya hana Mason Holgate cin wata kwallo da ya saka wa kai da kuma hari na-ci da Djibril Sidibe ya kai masa.

Masu masaukin bakin, Everton, sun karya lagon bakin nasu ne bayan Sidibe ya bai wa Calvert-Lewin kwallo a sama, inda shi kuma ya yi sufa ya saka ta a gidanta.

Nasarar ta dago Everton zuwa mataki na 13 sannan kuma wasan Premier na biyar kenan a jere ba tare da rashin nasara ba, inda Burnley ke samanta a mataki na 12.