Liverpool ta kara fintinkau a Premier bayan caskara Leicester 4-0

Roberto Firmino ne ya fara daga raga da ka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Roberto Firmino ne ya fara daga ragar 'yan Leicester City da ka

Liverpool ta kara bayar da tazara tare da tabbatar da matsayinta na kokarin daukar kofin Premier na bana, bayan da ta caskara mai bi mata baya Leicester City 4-0.

Kungiyar ta Jurgen Klopp ta fara wasan ne wanda aka yi a gidan Leicester (The King Power Stadium) da tazarar maki 10 tsakaninsu, da kuma kwantan wasa daya.

Roberto Firmino ne ya fara daga ragar masu masaukin da ka a minti na 31 bayan da Trent Alexander-Arnold ya aika masa wata bal.

Liverpool ta samu fanareti bayan da Caglar Soyuncu na Leicester ya taba bal da hannu, inda James Milner wanda aka yi canji ya shigo, ya ci da bugunsa na farko a wasan a minti na 71.

The Reds din sun kara cin ta uku bayan da Alexander-Arnold ya kara sanya wa Firmino wata bal, wadda ya ci a tsanake, a minti na 74, kafin shi ma dan bayan na Ingila ya ci tasa a minti na 78.

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Trent Alexander-Arnold ya bayar da bal an ci biyu, sannan kuma shi ma ya ci daya

Da wannan hanya da Liverpool suka kama ana ganin abu ne mai wuya a ce kungiyar ba ta dauki kofinta na Premier na farko ba a cikin shekara 30.

A yanzu maki biyu ne kawai Liverpool ta yi asara a wasanta 18 na farko a gasar, kuma ganin wasa daya kawai ta yi rashin nasara na Premie a bara, ba karamin rashin sa'a za ta gamu da shi ba, wannan dama ta cin kofin a bana ta kwace mata.

Jagorar ta Premier ta bayar da tazarar maki 13 tsakaninta da Leicester mai maki 39, a wasa 19.

Ita kuwa Manchester City da ke rike da kofin, wadda za ta bakunci Wolverhampton Wanderers ranar Juma'a a wasansu na mako na 19 tana da maki 38.

Wadanne wasanni kungiyoyin biyu za su yi nan gaba?

Leicester za ta je gidan West Ham ranar Asabar, 28 ga Disamba (karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya), yayin da Liverpool za ta karbi bakuncin Wolves washegari (karfe 5:30 na yamma agogon Najeriya da Nijar).

Sakamakon Sauran Wasannin na Alhamis

Tottenham 2-1 Brighton

Aston Villa 1- 0 Norwich City

Bournemouth 1- 1 Arsenal

Chelsea 0-2 Southampton

Crystal Palace 2-1 West Ham United

Everton 1-0 Burnley

Sheffiled United 1-1 Watford

Man United 4-1 Newcastle United