Guardiola ya hakura da kofin Premier

Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Guardiola ya ce "abin ya yi yawa"

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya fitar da rai da daukar kofin Premier bayan Wolves ta casa zakarun na Premier da ci 3-2 a daren jiya Juma'a.

City tana matsayi na uku a teburin Premier da tazarar maki 14 tsakaninta da jagorar teburin wato Liverpool, maki daya kuma tsakanijnta da Leicester City da ke mataki na biyu.

Da aka tambaye shi ko za su ci gaba da yunkurin lashe gasar, Guardiola ya shaida wa BBC 5 Live cewa: "Abin ya yi yawa, a'a."

City ta yi rashin nasara a wasa biyar na Premier a bana, wanda sau hudu kawai ta yi hakan a kakar wasan da ta gabata ta 2018-2019.

Kazalika City ta fi Liverpool yawan buga wasanni, wadda ita kuma maki biyu kacal ta barar a bana.

Liverppol din ta ci wasan Premier 26 cikin 27 kuma saura wasa biyu kacal ta kare shekarar ba tare da an ci ta ba a gasar.

"Ba zai yiwu mu rika tunanin Liverpool ba, tunanin Leicester muke yi," Guardiola ya bayyana.

"Muna da damar samun gurbi na biyu. Na san kwarewar 'yan wasana amma halin da ake ciki kenan yanzu."

Tuni Manchester City ta dauki kofin Community Shield bayan ta doke Liverpoool a bugun finareti a watan Agusta.

Har wa yau, tana buga gasar Zakarun Turai ta Champions League, inda za ta fafata da Real Madrid a zagayen 'yan 16 a watan Fabarairu mai zuwa.

Kazalika za ta buga wasan zagaye na uku na gasar FA Cup ranar 4 ga Janairu, kafin kuma ta fafata da Manchester United a wasan kusa da na karshe a kofin Carabao a ranar 7 ga watan Junairun dai.

Labarai masu alaka