Premier League: Ancelotti ya ci wasa biyu a jere a Everton

Carlo Ancelotti Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Calvert-Lewin ne ya ci wa Everton kwallonta biyu

Everton ta casa Newcastle har gida da ci 2-1 a wasan mako na 20 a gasar Premier.

Tun da farko Everton ce ta rike ragamar wasan a minti 45 na farko, kazalika har karshen wasan.

A minti na 13 ne dan wasan gaban Everton Dominic Calvert-Lewin ya jefa kwallo ta farko.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci kuma Fabian Schar ya farke wa Necastle kwallonta, inda wasa ya dawo kunnen doki.

Sai dai a minti na 64 Dominic Calvert-Lewin ya kara ta biyu, wadda kuma ta bai wa Everton din damar samun maki uku.

Wannan ce nasara ta biyu da Carlo Ancelotti ya yi a jere tun bayan karbar kungiyar da ya yi a hannun kocinta na rikon kwarya Duncan Ferguson.

Yanzu dai Everton za ta je bakunci Manchester City, kafin daga bisani ta je Anfield a wasan zagaye na uku na gasar FA tsakaninta da Liverpool.

Kungiyar dai yanzu na matsayi na 10 a teburi Premier da tazarar maki biyu tsakaninta da Crystal Palace da ke samanta a matsayi na tara.

Labarai masu alaka