Premier League: Tottenham ta yi canjaras da Norwich

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Finaretin da Harry Kane ya ci ne ya ceci Tottenham

Tottenham ta fuskanci koma baya a wasan Premier mako na 20 bayan kunnen dokin da ta yi da Norwich.

Finaretin da Harry Kane ya ci ne ya ceci Tottenham ta samu maki daya a filin wasa na Carrow Road, wanda hakan ya hana Norwich samun nasarar farko cikin wasa bakwai da ta buga na baya-bayan nan a Premier.

Mario Vrancic ne ya bude wasan da cin kwallo kafin hutun rabin lokaci, wadda ita ce kwallonsa ta farko a gasar Premier, kafin daga bisani Teemu Pukki ya ci ta biyu amma VAR ta hana.

Norwich ce ke jan ragamar wasan kafin daga bisani a sako Christian Eriksen, wanda ya farke kwallon da bugun tazara a minti na 55.

Minti shida tsakani dan bayan Tottenham Serge Aurier ya ci gida, hakan ya kara bai wa Norwich damar ci gaba da jan ragamar wasa.

Norwich ta ci gaba da samun dama kafin Dele Alli ya ci wata kwallo da alkalin wasa ya ce an yi satar gida.

Jim kadan kuma Harry Kane ya farke kwallon daya, bayan Christoph Zimmermann ya bige shi a yadi na 18.

Har yanzu dai Norwich na kasan teburi kuma tana bukatar maki shida ne kawai domin fita daga 'yan ukun karshe da za su iya fada wa gasar Championship.

Yayin da ita kuma Spurs ta koma matsayi na biyar da tazarar maki biyu tsakaninta da Chelsea da ke matsayi na hudu a teburin gasar.