West Ham ta kori kocinta Manuel Pellegrini

Manuel Pellegrini Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pellegrini ne koci na shida da aka kora a Premier

Manuel Pellegrini ya zama koci na shida da aka kora a Premier bana.

Korar Pellegrini ta zo ne bayan kashin da kungiyar ta sha da ci 2-1 a hannun Leicester City.

Wannan ne rashin nasara ta tara da kungiyar ta yi cikin wasa 12 da ta buga na baya-bayan nan.

Wannan dokewar da aka yi wa Hammers din ta janyo ta koma matsayi na 17, da tazarar maki daya kacal tsakaninta da kungiyoyi ukun karshen teburi.

An kori Pellegrini bayan kwashe wata 18 a bakin aiki, wanda aka ba shi a watan Mayun 2018 kan yarjejeniyar kwantaargin shekara uku.

Kungiyar karkashin jagorancinsa ta kare a matsayi na 10 a bara, Manuel Pellegrini ya zama koci na shida da aka kora a Premier bana.

Bugu da kari kan rashin kokarinta a Premier, an kuma yi waje rod da West Ham daga kofin Carabao tun a watan Satumba bayan dokewar da Oxford United ta yi mata da ci 4-0.