West Ham ta kori Pellegrini bayan ta sha kashi hannun Leicester

Kocin West Ham Manuel Pellegrini Hakkin mallakar hoto Getty Images

West Ham ta kori ta kori kocinta Manuel Pellegrini bayan ta sha kashi ci 2-1 a hannun Leicester City - rashin nasara karo na tara a wasanni 12.

West Ham yanzu tana matsayi na 17 a teburin Premier, maki daya tsakaninta da kasan tebur.

Pellegrini wanda West Ham ta dauka a watan Mayun 2018 kan kwantaragin shekaru uku, yanzu ya tafi bayan watanni 18.

West Ham ta sanar da korar shi bayan sa'a biyu da shan kashi hannun Leicester.

A farkon shekara West Ham za ta kara da Bournemouth kuma ba ta sanar da wanda zai maye gurbin Pellegrini ba.

Pellegrini yanzu shi ne koci na shida da aka kora a Premier a kakar bana.

Labarai masu alaka