Makomar Eriksen, Pogba, Richarlison, Moyes, da Giroud

Olivier Giroud Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United a shirye take ta jira har zuwa kammala kaka domin karbo dan wasan Tottenham dan kasar Denmark Christian Eriksen, mai shekara 27. (Sunday Telegraph)

Real Madrid ta shaidawa Zinedine Zidane cewa ya hakura da karbo Paul Pogba, mai shekara 26, daga Manchester United domin zai kawo cikas ga ci gaban matashin dan wasan tsakiya na Uruguay Federico Valverde, 21. (AS)

Sabon kocin Everton Carlo Ancelotti zai tsohe wa Manchester United kofar sayen dan wasan Brazil Richarlison, mai shekara 22, ko da kuma ta taya dan wasan fan miliyan £70. (Sun on Sunday)

David Moyes da Tony Pulis na daga cikin wadanda ake ganin za su maye gurbin Manuel Pellegrini da West Ham ta kora. (Sunday Telegraph)

Dan wasan Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 21, ya ce yana son ya kammala rayuwarsa a Liverpool. (Sportbladet, via Independent)

KocinJuventus Maurizio Sarri na son karbo dan wasan Faransa Olivier Giroud, mai shekara 33, daga Chelsea. (La Stampa - in Italian)

Bayern Munich, Juventus da Paris St-Germain na son sayen golan Jamus Marc-Andre Ter Stegen, mai shekara 27, daga Barcelona. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Sheffield United na son sayen matashin dan wasan QPRdan asalin Najeriya Eberechi Ezekan fan miliyan £12. (Sun on Sunday)

Barcelona ta ce koken da Arturo Vidal ya shigar kan ikirarin rashin biyansa kudaden lada, wani mataki na dan wasan na son komawa Inter Milan. (ESPN)

Fiorentina na son sayen dan wasan Manchester United Marcos Rojo, mai shekara 29. (La Nazione, via Football Italia)

Tsohon dan wasan Barcelona Andres Iniesta, mai shekara 35, ya yi watsi da tayin kungiyoyi Major League Soccer LA GalaxydaInter Miami da kuma Montreal Sounders inda ya nuna yana son ci gaba da taka leda a kulub dinsa na Japan Vissel Kobe. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Labarai masu alaka