Ebola da Bahagon Shagon 'Yansanda damben Mota
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An bai wa Shagon 'Yansanda mota a damben Dei-Dei

Kungiyar damben gargajiya ta kasa reshen babban birnin tarayya Abuja, Najeriya ta bai wa Bahagon Shagon 'Yansanda motar gasa.

An bai wa Bahago motar ne a daren Lahadi, bayan da Ali Zuma ya yanke cewar dan damben Jamus din ne ya kamata ya karbi mukullin motar.

Tun a safiyar Lahadi aka dambata tsakanin Abdurrazak Ebola daga Kudu da Bahagon Shagon 'Yansanda daga Arewa.

Turmi biyu suka taka babu kisa, amma Ebola ya yi raunin da sai da aka fitar da shi daga filin damben.

Hakan ne ya sa Ali Zuma ya ce ya bayar da minti biyu Ebola ya dawo filin wasa ko a bai wa Bahago mota, daga baya ya kara minti 10.

Daga baya Ebola ya koma fili bayan an duba lafiyarsa, sai dai an sa ran za a sake yin damben da yammaci a bai wa mai rabo mota.

Da yammacin kuma Ali Zuma ya kira shugaban Jaamawa da na Kudawa da na Guramada da su cimma matsaya.

Shi na Guramada ya ce duk abin da aka yanke ya amince, shi kuwa na Jamus ya ce su ya kamata a bai wa mota tun da Ebola bai koma fili a kan kari ba.

Na bangaren Kudawa kuwa cewa ya yi babu wanda ya gaya musu dokokin gasa cewar idan dan dambe bai dawo ba an cinye su, saboda haka a koma fili a ci gaba da dambe da yamma.

A yammacin kuwa ga Bahagon Shagon 'yansanda ga Ebola amma basui sake fafatawa ba. aka ci gaba da takaddama.

Daga baya ne Ali Zuma ya bai wa Bahagon Shagon 'Yansanda takardun mota da mukullinta a matsayin zakara.

Tun farko kungiyar dambe ta Abuja ta tsara damben rana daya na mota tsakanin Ebola da Bahago, duk wanda ya yi nasara a ba shi mota na biyu ya karbi Naira dubu 100.

Karon farko kenan da aka sa mota a damben gargajiya a rana daya a tarihin wasan a Najeriya.

An dambata ne a gidan wasa da ke Dei-Dei a Abuja, Najeriya.

Labarai masu alaka