David Moyes ya sake zama kocin West Ham

David Moyes Hakkin mallakar hoto Getty Images

West Ham United ta sanar da sake nada David Moyes a matsayin sabon kocinta

Moyes mai shekara 55 ya sanya hannu kan yarjejeniyar watanni 18 kuma shi zai jagoranci kungiyar a wasanninta na sabuwar shekara da za ta karbi bakuncin Bournemouth

Ya maye gurbin Manuel Pellegrini, wanda West Ham ta kora bayan ta sha kashi 2-1 a gida ranar Asabar a hannun Leicester.

Bayan shan kashi sau hudu a jere a gida, maki daya ne ya raba West Ham da 'yan kasan teburin Premier

Moyes tsohon kocin Everton da Manchester United ya taba horas da West Ham United a kakar 2017/18.

Labarai masu alaka