Chelsea ta kara yaga barakar Arsenal a Emirates

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Chelsea ta je har Emirates ta doke Arsenal da ci 2-1 a wasan mako na 20 a gasar cin kofin Premier da suka kara ranar Lahadi.

Arsenal ce ta fara cin kwallo a karawar ta hamayya ta hannun Pierre-Emerick Aubameyang tun kan a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka koma zagaye na biyu ne Chelsea ta farke ta hannun Jorginho, sannan ta kara na biyu ta hannun Tammy Abraham saura minti uku lokaci ya cika.

Chelsea za ta ziyarci Brighton & Hove Albion ranar Laraba 1 ga watan Janairun 2020, a ranar Arsenal za ta karbi bakuncin Manchester United..

Labarai masu alaka