Hamdallah ne kan gaba a cin kwallaye a 2019

Hamdallah Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan tawagar kwallon kafar Morocco, Abderrazak Hamdallah ya zama kan gaba a matakin wanda ya fi cin kwallaye a 2019, inda ya zuwa 57 a raga.

A ranar Asabar ne Hamdallah wanda ke taka leda a Al Nassr ta Saudi Arabia ya ci kwallo uku rigis a karawar da suka doke Al Feiha.

Hakan ne ya sa ya haura dan wasan Bayern Munich, Robert Lewandowski mai 54 da dan kwallon Barcelona, Lionel Messi wanda ya zura 50 a raga a 2019.

Mai shekara 29, wanda ya kafa tarihin cin kwallaye a gasar Saudi Arabia a shekarar nan, ya yi ritaya daga buga wa Morocco tamauila a watan Nuwamba, bayan da ba a ba shi goron gayyata zuwa tawagar ba.

Wasan karshe da Hamdalla ya yi wa Morocco shi ne a watan Yuni wanda suka yi rashin nasara da ci 1-0 a wasan sada zumunta da Gambia.

Labarai masu alaka