Man City za ta shiga shekara ta 2020 a ta uku a Premier

Man City Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester City ta yi nasarar cin Sheffield United da ci 2-0 a wasan mako na 20 a gasar cin kofin Premier da suka yi a Ettihad.

City ta fara cin kwallo ta hannun Sergio Aguero a minti na 53, bayan da ya samu kwallo daga hannun Kevin de Bryne.

De Bruyne ne ya kara na biyu a raga, bayan da ya samu kwallo ta hannu Riyad Mahrez.

Da wannan sakamakon City tana ta uku kenan a kan teburin Premier da maki 41, bayan da ta ci wasa 13 da canjaras biyu aka doke ta fafatawa biyar.

A ranar Juma'a ne City ta yi rashin nasara a hannun Wolves da ci 3-2, karawar da kungiyar ta fara cin kwallo biyu daga baya aka farke su.

Liverpool ce ta daya a kan teburi da maki 55, sai Leicester City ta biyu m,ai maki 42.

Labarai masu alaka