Liverpool ta bayar da tazarar maki 13 a teburi

Tawagar Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yanzu Liverpool ta bayar da tazarar maki 13

Liverpool ta kammala shekarar 2019 cikin jagorancin teburin Premier da maki 13 sakamakon nasarar da ta samu kan Wolves da ci daya mai ban haushi a filin wasa na Anfield.

An samu tsaiko a wasan sakamakon hukuncin da na'urar VAR ta rika yi a dukkanin kwallo biyu da bangarorin biyu suka jefa a raga.

Sadio Mane ne ya fara jefa kwallo kafin tafiya hutun ranbin lokaci amma sai da aka dakata na mintuna yayin da ake duba yiwuwar ko Lallana ya taba ta da da hannu kafin a ci.

Ita ma Wolves ta jefa tata kwallon amma VAR ta ce Jonny ya yi satar gida kafin Pedro Neto ya jefa kwallon bangaren dama na zaren Liverpool a mintin karshe na 45 din farko.

Liverpool ta kare shekarar ne a matsayin wadda ake ganin jiran shekara 30 da ta yi ba tare da kofin Premier ba ya zo karshe.

Ita ma Wolves ana ganin ta kare shekarar da kwarinta duk da rashin nasarar - tana mataki na bakwai da maki 30, a kasan Tottenham ita ma mai maki 30.

Labarai masu alaka