Shekara 10 da kai wa tawagar Togo hari a gasar Afcon ta 2010

"yan wasan Togo a bakin otel Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shekara 10 kenan da kai wa tawagar kwallon kafar kasar Togo hari yayin ake shirin fara wasan rukuni a gasar cin Kofin Kasashen Afirka ta 2010 a kasar Angola.

Wakilin BBC Matthew Kenyon ya tuna abin da ya faru a lokacin, yayin da yake shirin tattara wa BBC rahotanni game da gasar baki dayanta.

Kwanaki kadan kafin fara gasar cin Kofin kasashen Afirka ta 2010, tawagar kasar Togo tana cikin shauki. Sun dawo cikin gasar bayan da suka gaza shiga a 2008, suna kokarin karawa da wasu daga cikin manyan tawagogi a gasar.

Matsugunin tawagar ta Togo yana garin Pointe Noir na kasar Congo ne - fiye da kilomita 100 daga filin wasan da za su buga wasannin rukuninsu a garin Cabinda.

Garin Cabinda a rabe yake da sauran sassan Angola. Maimakon su shiga jirgin sama zuwa babban birnin Luanda sannan su karasa Cabinda, tawagar sai ta zabi ta tafi a mota.

A wani yammaci, wasu 'yan wasan ma har sun fita yawo cikin gari - abin da ya bata ran kocinsu - tawagar ta kama hanyar zuwa kan iyaka tare da 'yan wasa suna kakaci da shewa a tsakaninsu.

"Muna tsaka da nishadin mu bayan mun haura iyaka, wasu daga cikinmu suna sauraron kida. Ina tuna cewa bayan tafiyar minti 15 sai muka fara jin harbin bindiga a daji - sai muka sa dariya - a lokaci guda kuma abubuwa suka rikice," dan wasan tsakiya Junior Senaya ya bayyana.

Har sai da aka raunata wasu ma kafin wani ya san me yake faruwa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Senaya ya tuna mai magana da yawun tawagar, Stanislas Ocloo, yana tsaye domin daukar bidiyon isowar tawagar a Angola a lokacin - nan take aka harbe shi kuma ya mutu.

Shi ma mai tsaron raga Kodjovi Obilale yana tuna abin da ya faru. Cikin kankanin lokaci rayuwarsa ta sauya bayan ya gano cewa shi ma an harbe shi.

"Na ji karar bindiga (mashinga),"in ji shi, "daga sanda na mike don na tsere sai kawai na ji kamar an daure ni a jikin kujerar.

"A sannan ne na ga jini na zuba daga cikina da bayana. Nan take kuma na firgita na ce: 'An harbe ni, ku taimake ni, ku taimake ni, ina son ganin 'yata da dana. Ba na son na mutu."

Tawagar ba ta iya tserewa dahga harin ba saboda shi kansa direban motar - Mario Adjoua - an jikkata shi tun daga farkon lamarin.

Shi ma shahararren fdan wasa Adebayor ya bayyana abin da ya faru a minti 30 mafi muni a rayuwarsa.

"Ba wai mutum daya ne yake harbi kan motar tamu ba," ya fada mani bayn 'yan wasan sun samu kan su a wani otel.

"Mun kasance a tsakiyar rikicin tsawon kusan miti 30 ko ma sama da haka. Aka tsare motarmu sannan aka yi ta harbi a kanta. Maganar gaskiya wannan na daya daga cikin abu, mafi muni da zan gani a rayuwata.

"Ba don jami'an tsaro ba da ba zan iya magana da kai ba yanzu. Babu mamaki da gawata za ka yi magana."

Labarin yadda abin ya kawo karshe ya sha bamban - Adebayor ya ce wani rukunin motocin 4x4 ne suka iso domin ceton 'yan wasan a lokacin da ake tsaka da harbe-harben, shi kuma Senaya ya ce shuru kawai ya ji.

Daga karshe dai an kai su asibiti baki dayansu a wajen garin Cabinda City, inda aka ba su kulawa.

"A irin wannan lokacin ne za ka gane mai ya faru a lokacin da na kalli idanun 'yan wasan," Adebayor ya fada.

"Bayan na fito na ga kowa yana kuka, suna ta magana kan iyalansu, suna kiran iyayensu a waya.

"Ina ganin wannan ne lokaci mafi muni a wannnan ranar saboda a nan za ka ji yadda mutane ke barin wasiyya saboda sun za ci mutuwa za su yi."

A karshe sun karasa zuwa masaukinsu tare da wadanda suka rasu da kuma masu rauni ba tare da wasu jami'an tsaro ba.

A lokacin ne na hadu da su sannan muka shiga ciki tare da su.

Duka kungiyoyi hudun da suke rukuni daya da Togo sun a zauna ne a otel daya. Kolo Toure da wasu 'yan Ivory Coast suka fito domin nuna alhininsu - tuni jita-jita ta yadu.

Kowa ya yi shuru yayin da 'yan wasa ke cin abincin dare. A lokacin ne cikin fushi Adebayor ya bayyana wa BBC abin da ya faru.

Jim kadan bayan harin, wata kungiya ta dauki nauyin kai harin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A karshe dai gwamnatin kasar Togo ta kira 'yan wasanta gida domin yin jana'izar wadanda suka rasu da kuma yin makokin kasa baki daya.

Wannan matakin ya jawo wa tawagar hukuncin haramta mata shiga harkokin wasanni na wani dan lokaci daga hukumar Caf saboda "katsalandan din gwamnati" a harkar kwallon kafa.

Labarai masu alaka