Tottenham za ta dauki Gedson Fernandes

Fernandes Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Litinin Tottenham za ta gwada koshin lafiyar dan wasan Benfica, Gedson Fernandes.

Fernandes zai buga wasannin aro a Tottenham mai buga gasar Premier zuwa wata 18.

West Ham tana zawarcin dan wasan ruwa a jallo, amma Fernandez ya amince ya yi aiki karkashin Jose Mourinho.

Idan har Tottenham ta dauki dan wasan, zai zama na farko da ya je kungiyar karkashin Mourinho.

An fahimci cewar Tottenham za ta iya sayen dan kwallon idan har ya taka rawar gani, bayan cikan yarjejeniya.

Zuwa Fernandes Totenham zai taimakawa kungiyar, bayan da Harry Kane da Moussa Sissoko ke jinya.

Labarai masu alaka