Man United za ta sayi Bruno Fernandes

Fernandes Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United da Sporting Lisborn sun tattauna kan cinikin Bruno Fernandes kan fam miliyan 60.

Fernandes, mai buga wasa tsakiya, mai shekara 25 ya ci kwallo biyu a karawar da Sporting ta doke Vitoria Setubal 3-1 ranar Asabar a gasar Portugal.

Dan wasan na tawagar Porugal na son zuwa Manchester United, sai dai kawo yanzu kungiyar ba su kai ga cimma yarjejeniya ba.

Kocin United, Ole Gunnar Solskjaer da mataimakinsa, Mike Phelan sun kalli wasan Fernandes a lokacin da Sporting ta fafata da FC Porto ranar 5 ga watan Janairu.

United na hangen gurbin masu buga wasan tsakiya take da matsala, nan ya kamata ta bunkasa.

Kungiyar ta Old Trafford tana ta biyar a teburin Premier da tazarar maki biyar tsakaninta da Chelsea a kokarin neman gurbin Champions League na badi.

Labarai masu alaka