Zidane gwarzon lashe wasan karshe

Zidane Hakkin mallakar hoto Getty Images

Zinedine Zidane ya dauki kofi 10 a Real Madrid, tara daga ciki ya lashe bayan wasan karshe da na La Liga da ya dauka a kakar 2016/17.

Zidane ya fara da jan Real wasan karshe a gasar Champions League a 2016, inda ya yi nasara a kan Atletico Madrid a bugun fenariti a birnin Milan.

'Yan watanni tsakani kocin ya cinye Sevilla 3-2 a wasan karshe na UEFA Super Cup, sannan ya kara da kofin Zakarun nahiyoyin duniya, bayan doke Kashima Antlers.

Daga nan ne Zidane ya dauki kofin La Liga na kakar 2016/17, sannan ya yi nasara a kan Juventus da ci 4-1 ya lashe Champions League a Cardiff a 2017.

Haka kuma kocin ya doke Manchester United a UEFA Super Cup, sannan ya yi nasara a kan Barcelona gida da waje ya dauki UEFA Supercopa de Espana a 2017.

Daga nan ne ya kara daukar kofin Zakarun nahiyoyin duniya, bayan da ya casa Gremio.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Zidane ya lashe kofin Zakarun Turai na uku a jere a Real, bayan da ya yi nasarar cin Liverpool a wasan da suka yi a Kiev.

'Yan kwanaki tsakani Zidane ya sanar cewar ya ajiye aikin don radin kansa zai kuma huta dan wani lokaci.

Daga baya kocin ya sake karbar aikin, inda ake ta shakku ko zai tabuka a Santiago Bernabeu kamar yadda ya yi baya?

Sai dai kuma Zidane ya bai wa marada da kunya, inda ya lashe Spanish Super Cup, bayan da ya yi nasara a kan Atletico a bugun fenariti.

Kawo yanzu Real Madrid tana ta biyu a gasar cin kofin La Liga, sannan tana cikin Champions League da sauran wasannin da ake sa ran kocin zai taka rawar gani.

Labarai masu alaka