Copa del Rey: Unionistas da Real Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar kwallon kafar Spaniya ta bayyana jadawalin Copa del Rey na kungiyoyi 32 da za su fafata a bana.

Cikin jadawalin Real Madrid za ta ziyarci Unionistas de Salamanca, ita ma Barcelona za ta je gidan Ibiza.

Wadan da suke buga gasar La Liga ne za su fara ziyartar wadan da ke buga karamar gasar da ke bin ta La Liga.

Kuma dun wanda aka ci sai dai ya wanke riga, kuma dole sai an samu zakara a ranar.

Sai a karawar daf da karshe aka yin wasannin gida da waje a gasar ta Copa del Rey.

An tsayar da cewar za a fara wasannin ne tsakanin 21 zuwa 23 ga watan Janairu.

Idan har Madrid ta yi nasara za ta buga wasan gaba na kungiyoyi 16 da za su rage a wasannin mako daya tsakani.

Za a buga wasan daf da na kusa da na karshe ranar 5 ga watan Fabrairu, sannan fafatawar daf da karshe da za a yi gida da waje tsakanin 12 ga watan Fabrairu da 4 ga watan Maris.

Za a buga wasan karshe a Copa del Rey na bana ranar 18 ga watan Afirilu.

Yadda aka raba jadawalin Copa del Rey

 • Ibiza da Barcelona
 • Logrones da Valencia
 • CYD Leonesa da Atletico Madrid
 • Unionistas de Salamanca da Real Madrid
 • Ebro da Leganes
 • Badajoz da Eibar
 • Badalona da Granada
 • Recre Huelva da Osasuna
 • Rayo Vallecano da Real Betis
 • Mirandes da Celta Vigo
 • Tenerife da Real Valladolid
 • Girona da Villarreal
 • Elche da Athletic Club
 • Real Zaragoza vs Real Mallorca
 • Sevilla da Levante
 • Real Sociedad da Espanyol

Labarai masu alaka