Hernandez zai koma Amurka da taka leda

Hernandez Hakkin mallakar hoto Getty Images

LA Galaxy mai buga gasar Amurka na son sayen tsohon dan kwallon Manchester United, Javier Hernandez.

Dan kasar Mexico, mai shekara 31, baya buga wasa sosai a Sevilla, bayan da ya koma can daga West Ham United.

An dade ana hangen buga gasar Amurka ce makomar Hernandez, kuma zai kara daga martabar wasannin.

LA Galaxy tana da gurbin da Hernandez zai buga mata tamaula, bayan da yarjejeniyar Zlatan Ibrahimovic ya kare a karkshen kakar kwallon Amurka.

Hernandez wanda ya lashe kofin Premier biyu a United ya buga tamaula aro a Real Madrid.

Labarai masu alaka