Barcelona ta kori kocinta Ernesto Valverde kuma ta nada Quique Setien

Ernesto Valverde Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ta dauko Ernesto Valverde ne daga Athletic Bilbao a 2017

Barcelona ta sallami kocinta Ernesto Valverde tare da maye gurbinsa da tsohon kocin Real Betis Quique Setien.

Valverde, mai shekara 55, ya taimakawa Barcelona lashe kocin La Liga biyu a jere, kuma shi ke saman tebur da yawan kwallaye a bana.

Sai dai Barcelona ta fuskanci koma baya karkashinsa inda ta kasa lashe kofin zakarun Turai.

Setien, mai shekara 61, ya taimakawa Betis zuwa matsayi na shida a teburin La liga a 2005 da kuma zuwa wasan dab da karshe a Copa del Rey kafin ajiye aikinsa a watan Mayu.

Ya amince da yarjejeniyar shekaru biyu da rabi kuma a gobe Talata ne Barcelona za ta gabatar da shi ga 'yan jarida.

A cikin sanarwar da ta fitar, Barcelona ta ce Valverde ya amince ya kawo karshen aikinsa tare da gode masa kan kwarewarsa da kuma jajircewarsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Betis Quique Setien zai maye gurbin Ernesto Valverde

Valverde ya fuskanci matsin lamba musamman a karshen kakar da ta gabata bayan kashin da Barcelona ta sha a gidan Liverpool duk da ta ci 3-0 a karawar farko, sannan da rashin nasarar da ta yi wasan karshe na lashe Copa del Rey a hannun Valencia.

Wasu na ganin yadda Liverpool ta casa Barcelona, kocin ya kasa gano inda matsalar take, bayan Roma ta fitar da Barcelona kafin Liverpool.

Labarai masu alaka