Barcelona ce kan gaba a samun kudi a Turai

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images

A karon farko Barcelona ce ta daya wajen samun kudi a nahiyar Turai a bara a wani bincike da aka gudanar.

Kungiyar ta Spaniya ta samu kudin shiga da ya kai Fam miliyan 741.1 a kakar 2018/19 in ji Deloitte, kamfanin da ke sa ido kan kashe-kashen kudi a fanni tamaula.

Real Madrid ta daya a baya ta koma ta biyu, bayan da ta samu kudin shiga da ya kai fam miliyan 667.5, inda Manchester United ke mataki na uku mai fam miliyan 627.1.

An kuma yi hasashen cewar United za ta rasa gurbinta na wadda take ta daya a samun kudi a Premier a shekara mai zuwa.

Jerin wadan da ke kan gaba a samun kudi a 2018/19

 • 1Barcelona 741.1
 • 2Real Madrid 667.5
 • 3Manchester United 627.1
 • 4Bayern Munich 581.8
 • 5Paris St-Germain 560.5
 • 6Manchester City 538.2
 • 7Liverpool 533
 • 8Tottenham 459.3
 • 9Chelsea 452.2
 • 10Juventus 405.2
 • 11Arsenal 392.7
 • 12Borussia Dortmund 332.4
 • 11Atletico Madrid 324
 • 14Inter Milan 321.3
 • 15Schalke 286.3
 • 16Roma 203.6
 • 17Lyon 194.6
 • 18West Ham 190.7
 • 19Everton 187.7
 • 20Napoli 182.8

Labarai masu alaka