Arteta zai yi aron Stones, Dangote zai sayi Arsenal

Eriksen Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kocin Arsenal, Mikel Arteta na duba yiwuwar aron mai tsaron bayan Manchester City, John Stones in ji Sun.

Atletico Madrid ta cimma yin zawarcin dan kwallon tawagar Faransa da Arsenal, Alexander Lacazette, idan hakan bai yi wu ba ta koma neman dan wasan Paris St Germain, Edison Cavani in ji Express.

Kungiyar Liverpool ba ta amince ta bai wa Roma aron Xherdan Shaqiri kamar yadda Star ta wallafa.

Ita kuwa Guardian cewa ta yi kocin Newcastle United, Steve Bruce zai zauna da mai kungiyar Mike Ashley don jin ko da wani shiri a lokacin nan da ake cin kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo da take ci.

Southampton ta kara nana ta cewar ba za ta sayar da dan kwallonta Che Adams ba, babu batun bai wa Leeds aro kuma in ji Mirror.

Attajirin mai kudi dan Najeriya, Aliko Dangote, mai shekara 62 ya ce yana fatan sayen Arsenal a shekarar 2021 kamar yadda Evernin Stardard ta wallafa.

Telegraph ta wallafa cewar Pep Guardiola zai bai wa 'yan wasan Manchester City hutun mai tsawo idan an kammala gasar Premier ta bana.

Labarai masu alaka