Tottenham ta dauki aron Gedson Fernandes

Fernandes Hakkin mallakar hoto Getty Images

Gedson Fernandes ya koma Tottenham daga Benfica da zai buga wa wasannin aro zuwa wata 18.

Mai shekara 21, ya fara yi wa Benfica wasa a kakar bara, an kuma bai wa Spurs zabin sayen dan kwallon idan ya taka rawar gani a kungiyar.

Fernandes ya ci kofin gasar Portugal a Benfica a bara, bayan da ya buga mata wasa 53, ya ci kwallo biyu a Champions League.

Shi ne dan wasa na farko da ya je Tottenham tun bayan da ta bai wa Jose Mourinho aikin kocinta.

Fernandes, wanda ya buga wa tawagar kwallon kafar kafar Portugal wasa biyu, ya ce tuni iyalansa suna Landan domin taya shi zama.

Dan wasan ya koma Tottenham a lokacin da Moussa Sissoko da Tanguy Ndombele da Harry Kane ke jinya, yayin da ba a san makomar Christian Eriksen ba.

Rawar da Fernandes ya taka a gasar League a Portugal

Wasannin da ya yi 29

Wasannin da aka fara da shi 13

Kwallayen da ya ci 0

Taimakawa a ci kwallo 2

Samar da damarmaki 7

Labarai masu alaka