Liverpool za ta lashe kyautar bajinta biyu

Liverpool Hakkin mallakar hoto PA Media

Liverpool tana daga cikin wadan da za su lashe kyautar Laureus ta wasannin duniya.

Ana sa ran Liverpool za ta ci kyautar kungiyar da ba kamarta a 2019, da wadda aka ci a wasa ta dawo ta farke ta kuma yi nasara.

Kungiyar ta Anfield wadda ta lashe kofin Zakarun Turai na Champions League tana daga cikin guda shida da ke takarar wadda ta fi yin fice a bara.

Andy Murray mai buga kwallon tennis an ba shi kyautar wanda ya yi jinya mai wuyar sha'ani, sannan ya dawo fagen fama.

Lewis Hamilton yana cikin masu takarar gwarzon mai wasa da ba kamarsa a 2019, bayan da ya lashe tseren motocin Formula 1 karo na shida.

haka shima Tiger Woods yana cikin takara, bayan da ya ci babban kofin kwararru a kwallon golf na 15 a cikin watan Afirilu.

Mai wasan lankwasa jiki, Simone Biles na fatan lashe kyauta ta uku ta gwarzuwar wasa a bara, inda take yin takara da mutum shida.

Ciki har da 'Yar Amurka mai taka leda wadda ta lashe kyautar takalmin zinare a gasar cin kofin duniya a kwallon mata da aka yi a Faransa.

Haka kuma dan damben boksin, Andy Ruiz na cikin wadan da suka haskaka a 2019, bayan da ya doke Anthony Joshua ranar 1 ga watan Julin 2019.

Mutum 68 ne mambobin cibiyar bayar da kyautar a fannin wasannin duniya mai suna Laureus ne za su fidda gwanaye ranar 17 ga watan Fabrairu.

Jerin kyautukan da za a lashe

Gwarzon dan wasa

 • Lewis Hamilton (Burtaniya) - Formula 1
 • Eliud Kipchoge (Kenya) - tsalle-tsalle da guje-guje
 • Marc Marquez (Spain) - tseren babur
 • Lionel Messi (Argentina) - kwallon kafa
 • Rafael Nadal (Spain) - kwallon tennis
 • Tiger Woods (Amurka) - kwallon golf

Gwarzuwar 'yar wasa

 • Simone Biles (Amurka) - lauya jiki
 • Allyson Felix (Amurka) - tsalle-tsalle da guje-guje
 • Shelly-Ann Fraser-Pryce (Jamaica) - tsalle-tsalle da guje-guje
 • Naomi Osaka (Japan) - kwallon tennis
 • Megan Rapinoe (Amurka) - kwallon kafa
 • Mikaela Shiffrin (Amurka) - zamiyar kankara

Kungiya mafi shahara

 • Liverpool FC (Burtaniya) - kwallon kafa
 • Mercedes-AMG Petronas (Jamus) - tseren motoci
 • Tawagar Afirka ta Kudu ta zari ruga
 • Tawagar kwallon kwandon Spaniya
 • Toronto Raptors (Canada) - kwallon kwando
 • Tawagar kwallon kafa ta mata ta Amurka

Wanda ya yi bajinta

 • Bianca Andreescu (Canada) - kwallon tennis
 • Egan Bernal (Colombia) - tseren kekuna
 • Coco Gauff (Amurka) - kwallon tennis
 • Tawagar kwallon zari ruga ta Japan
 • Andy Ruiz Jr (Amurka) - damben boksin
 • Regan Smith (Amurka) - linkaya

Wanda aka cire tsammani, amma ya yi fice

 • Nathan Adrian (Amurka) - linkaya
 • Sophia Florsch (Jamus) - tseren motoci
 • Christian Lealiifano (Australia) - kwallon zari ruga
 • Kawhi Leonard (Amurka) - kwallon kwando
 • Liverpool FC (Burtaniya) - kwallon kafa
 • Andy Murray (Burtaniya) - kwallon tennis

Dan wasa da ya taka rawar gani mai bukata ta musamman

 • Omara Durand (Cuba) - tsalle-tslalle da guje-guje
 • Diede de Groot (Netherlands) - kwallon tennis a keken guragu
 • Oksana Masters (Amurka) - zamiya da tseren keke
 • Jetze Plat (Netherlands) - tseren keke
 • Manuela Schar (Switzerland) - tseren keken guragu
 • Alice Tai (Burtaniya) - linkaya

Labarai masu alaka