West Ham ta sake daukar Randolph

Randolph Hakkin mallakar hoto Getty Images

West Ham ta sake daukar mai tsaron ragar tawagar Jamhuriyar Ireland ta Arewa, Darren Randolph.

Randolph ya koma West Ham daga Middlesbrough mai buga gasar Championship kan fam miliyan hudu.

Dan wasan ya kama gola sau 42 a Hammers tsakanin 2015 zuwa 2017, sannan ya koma Boro kan fam miliyan biyar.

Randolph ya koma West Ham ne, bayan da Lukasz Fabianski ke jinya.

Fabianski, mai shekara 34, ya ji rauni a lokacin da zai buga kwallo a karawar da West Ham ta yi rashin nasara a gasar Premier a gidan Sheffield United.

Rabon da Randolph ya kama gola tun 24 ga watan Nuwamba, sakamakon jinya da ya yi, sai dai ana sa ran zai kama gola a gasar Premier a karshen mako da Everton.

Labarai masu alaka