Inter za ta dauki Spinazzola ta bayar da Politano

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Inter Milan na shirin daukar mai tsaron bayan Roma, Leonardo Spinazzola, ita kuma ta bayar da Matteo Politano.

A ranar Laraba ne likitocin Inter suka duba koshin lafiyar Spinazzola.

Kocin Inter ya koma zawarcin Spinazzola ne, bayan da Manchester United ba ta amince Ashley Young ya bar kungiyar a bana ba.

Zuwan Spinazzola Inter na dakushen damar zuwan Young Italiya a kakar nan.

Karshen kakar da muke ciki kwantiragin Young, mai shekara 34, zai kare a Manchester United.

Politano, mai shekara 26, zai koma Roma da taka leda kungiyar da ya fara murza leda a matsayin kwararren dan kwallo a karamar kungiya, sannan ya koma Perugia da Pescara da kuma Sassuola.

Inter ta ci gaba da zawarcin dan kwallon Tottenham, Christian Eriksen da dan wasan Chelsea, Olivier Giroud.

Conte ya san hazakar 'yan kwallon da suka nuna a lokacin da ya horas a Chelsea, yana kuma ganin rawar da za su taka a gasar Serie A.

Labarai masu alaka