Kamaru ta sauya ranakun gasar kofin nahiyar Afirka

Cup of Nations Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar kwallon kafar Kamaru Fecafoot ta sanar da ranar 9 ga watan Janairu domin fara gasar cin kofin nahiyar Afirka da za ta karbi bakunci a 2021.

Tun farko ana yin gasar a tsakanin Yuni da Yuli, amma Kamaru ta ce dole ne a sauya lokacin, sakamakon yanayi na damuna a lokacin Yuni da Yuli.

Mahukuntan hukumar kwallon kafar Kamaru ne suka zauna da na hukumar kwallon kafar Afirka CAF, har da shugabanta Ahmad da suka yi ranar Laraba a Yaounde.

Haka kuma sauyin ba zai yi karo da kalandar gasar kofin duniya na zakarun nahiyoyi da za a yi a China a watan Yunin 2021.

A watan Nuwamberr 2018 ne hukumar kwallon kafar Afirka ta kwace izinin karbar bakuncin gasar 2019, sakamakon jan kafa wajen shirye-shiryen gudanar da wasannin..

Wata daya tsakani CAF ta bayar da sanarwar Kamaru ta amince ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka a 2021.Kamaru ta sauya ranar gasar kofin Afirka

Labarai masu alaka