PSG da Inter na neman Eriksen

Solskjaer Hakkin mallakar hoto Getty Images

Leicester City ta tambayi Manchester United idan za a sayar mata da mai tsaron baya Luke Shaw, saboda tana ganin Ben Chilwell zai koma Chelsea in ji Mail.

Paris St-Germain za ta yi rige-rigen daukar dan kwallon Tottenham, Christian Eriksen, wanda Inter Milan ke zawarci in ji Mirror.

Ita kuwa Marca cewa ta yi babban jami'in Atletico Madrid, Miguel Angel Gil Marin yana Paris domin tattaunawa da PSG kan sayen Edison Cavani.

Manchester Everning Starndard kuwa cewa ta yi Manchester City ta sanar da Arsenal cewar ba za ta sayar mata da mai tsaron baya, John Stone ba.

The Sun kuwa cewa ta yi Manchester United sai ta biya Ole Gunnar Solskjaer fam miyan biyar idan har za ta sallameshi ba tare da kwantiraginsa ya kare ba.

Star kuwa ta wallafa cewar Olivier Giroud na daf da komawa Inter Milan, bayan da Chelsea ke neman fam miyan shida kudin dan wasan mai shekara 33.

Labarai masu alaka