Firimiyar Najeriya: Katsina da Pillars sun yi 1-1

nIGERIAN pREMIER Hakkin mallakar hoto NPFL

Katsina United da Kano Pillars sun tashi 1-1 a wasan mako na 15 a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya da suka kara ranar Laraba.

Pillars ce ta fara cin kwallo ta hannun Seun Adelani Yusuf a minti na 34 da fara wasa daga baya Katsina ta farke ta hannun Tasiu Lawal daf da za a je hutu.

Kawo yanzu Katsina ta hada maki 20, bayan wasa 14, ita kuwa Pillars mai kwantan wasa biyu tana da makinta 16.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi:

Wolves 1-2 Rangers

Abia Warriors 2-1 FC Ifeanyiubah

Rivers United 2-1 Lobi Stars

Sunshine Stars 2-1 Plateau United

Enyimba 0-2 Heartland

Akwa United 0-2 Kwara United

MFM 2-1 Jigawa Golden Stars

Labarai masu alaka