'Yan Premier da za su buga kofin Afirka a 2021

Algeria

Bayan da aka yanke shawarar sauya lokacin buga gasar kofin nahiyar Afirka zuwan watan Janairu za a samu sama da 'yan wasan Premier 30 da ba za su buga wa kungiyoyinsu wasa shida ba.

Algeria ce ta lashe kofin da aka yi a Masar tsakanin Yuni zuwa Yulin shekarar 2019, amma za a buga gasar 2021 daga Janairu zuwa Fabrairu.

'Yan wasan da ke Liverpool Sadio Mane na Segegal da Mohamed Salah na Masar da Naby Keita na Guinea za su buga wa tawagoginsu wasanni idan sun samu gurbi.

Hakan na nufin 'yan wasan ba za su buga wa Liverpool wasa shida ba tsakanin Janairun zuwa Fabrairu, ya dangan ta da kokarin kakashensu a gasar.

Jerin 'yan kwallon Afirka da ke buga Premier da ake sa ran za su buga kofin nahiyar Afirka idan kasashensu sun samu gurbin shiga gasar 2021..

Arsenal - Pierre-Emerick Aubmaeyang (Gabon), Nicolas Pepe (Ivory Coast), Mohamed Elneny (Masar- wasannin aro a Besiktas)

Aston Villa - Marvelous Nakamba (Zimbabwe), Trezeguet (Masar), Jonathan Kodjia (Ivory Coast), Ahmed Elmohamady (Egypt)

Brighton - Leon Balogun (Nigeria), Yves Bissouma (Mali), Gaetan Bong (Cameroon), Percy Tau (Afirka ta Kudu- wasannin aro a Club Brugge)

Crystal Palace - Jeffrey Schlupp (Ghana), Cheikhou Kouyate (Senegal), Jordan Ayew (Ghana), Wilfried Zaha (Ivory Coast)

Everton - Alex Iwobi (Nigeria), Jean-Philippe Gbamin (Ivory Coast), Oumar Niasse (Senegal), Yannick Bolasie (DR Congo - wasannin aro a Sporting Lisbon)

Leicester City - Kelechi Ịheanachọ (Nigeria), Wilfred Ndidi (Nigeria), Daniel Amartey (Ghana), Islam Slimani (Algeria - currently on loan at Monaco), Rachid Ghezzal (Algeria - currently on loan at Fiorentina)

Liverpool - Naby Keita (Guinea), Mohamed Salah (Egypt), Sadio Mane (Senegal). Joel Matip (Cameroon) has retired from international football.

Manchester City - Riyad Mahrez (Algeria)

Manchester United - Eric Bailly (Ivory Coast)

Newcastle - Christian Atsu (Ghana), Henri Saivet (Senegal)

Southampton - Moussa Djenepo (Mali), Sofiane Boufal (Morocco), Mario Lemina (Gabon - currently on loan at Galatasaray)

Tottenham - Victor Wanyama (Kenya), Serge Aurier (Ivory Coast)

Watford - Isaac Success (Nigeria), Ismaila Sarr (Senegal)

West Ham - Arthur Masuaku (DR Congo)

Wolves - Romain Saiss (Morocco)

Labarai masu alaka