Da kyar Rashford ya fuskanci Liverpool

Rashford Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ole Gunnar Solskjaer ya ce ya yi ganganci da ya saka Rashford a wasan FA da United ta ci Wolves 1-0 ranar Laraba.

Rashford, mai shekara 22, sai sauya shi aka yi saura minti 10 a tashi wasa, bayan da ya yi minti 16 ana duba raunin da ya ji a gadon baya.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Ingila ya ci kwallo 22 a kakar bana a Manchester United da kasarsa.

Solskjaer ya ce bai kamata ya sa Rashford a wasan Wolves ba, ganin fafatawar da zai yi da Liverpool ranar Lahadi a Anfield a gasar Premier.

Bayan da United ta yi nasara a kan Wolves, yanzu za ta fafata da Watford ko kuma Tranmere ranar 26 ga watan Janairu a wasan zagaye na hudu.

United tana mataki na biyar a kan teburin Premier, tana kuma cikin gasar Europa Cup ta kungiyoyi 32 da suka rage, sannan za ta gidan Manchester City wasa na biyu a Caraboa Cup.

A fafatawar farko da suka buga a Old Trafford, City ce ta yi nasara da ci 3-1.

Labarai masu alaka