Ramos da Marcelo sun ci kofi 42 a Real Madrid

Ramos Marcelo Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos da mataimakinsa Marcelona sun lashe kofi 21 kowannensu a Real Madrid.

A ranar Lahadi Real Madrid ta ci kofin Spanish Super Cup, bayan da ta doke Atletico Madrid da ci 4-1 a bugun fenariti, kuma na 21 da kowannensu ya ci.

'Yan wasan sun fara da daukar kofin La Liga a 2006/07, sannan suka kara yin bajintar a kakar gaba.

Daga nan sun kara lashe La Liga tare a 2011/12 da kuma 2016/17.

Ramos da Marcelona sun ci Champions League hudu, kuma sun zura kwallo a raga a wasan karshe da Atletico a Lisborn a 2014.

Ramos ne da kansa ya daga kofin da kungiyar ta lashe a 2016 da 2017 da kuma na 2018, ya kuma ci kwallo a kofin La decima da Real ta hada.

Ramos da Marcelona sun lashe kocin duniya na zakarun nahiyoyi a 2014 da 2016 da 2017 da kuma 2018, inda Madrid ta zama zakara.

Haka kuma 'yan kwallon sun lashe kofin zakarun Turai da na Spanish Super Cups.

Real ta lashe Spanish Super Cup hudu a 2014 da 2016 da 2017 da kuma wanda ta yi a Saudi Arabia.

Jumulla Ramos da Marcelo kowanne ya ci kofi 21 a Real Madrid da ya hada da Champions Leagues hudu da Club World Cups hudu.

Sautran sun hada da European Super Cups uku da kofin LaLiga hudu da Copa del Rey biyu da kuma Spanish Super Cups hudu.

Labarai masu alaka