Premier League: Man United ta dauki Ighalo na Najeriya

Odion Ighalo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ighalo ya ci kwallo 39 a Premier a 2014 zuwa 2017

Manchester United ta dauki dan wasan gaban tawagar Super Eagles ta Najeriya wato Odion Ighalo daga kungiyar Shanghai Shenhua ta China a matsayin aro.

Babu zabin sayen dan wasan mai shekara 30 a cikin yarjejeniyar daukar tasa idan ya gama zamansa zuwa karshen kakar bana.

Ighalo wanda har yanzu yake China amma ake tsammanin zai isa Ingila a 'yan kwanaki kadan, ya ci kwallo 39 a wasa 99 a Premier lokacin da ya buga wa Watford wasa a 2014 zuwa 2017.

"Odion kwararren dan wasa ne," in ji Ole Gunnar Solskjaer.

"Zai zo ya ba mu damar zabi tsakanin 'yan wasan gabanmu a dan lokacin da zai kasance tare da mu.

"Kwararren dan wasa mai hazaka, zai yi amfani da damar da ya samu."

Ighalo ya koma buga gasar Chinese Super League ta kasar China a 2017, a kungiyar Changchun Yata.

Bayan kaka biyu kuma sai ya koma Shanghai Shenhua duk a China, inda ya ci kwallo 10 a wasa 19.

Hazakar da ya nuna a tawagar Najeriya ta sa ya burge jama'a, yayin da ya fi kowa zira kwallo a wasannin cancantar shiga gasar cin Kofin Kasashen Afirka da kwallo bakwai, sannan kuma ya ci biyar a gasar ta 2019.

Wasu kungiyoyin na Premier sun neme shi amma Ighalo ya fi son ya taka wa United leda.

Shi ne babban dan wasa na biyu da United din ta karbo aro tun bayan Radamel Falcao a 2014, wanda ya je daga Monaco.