Premier League: Chelsea da Leicester sun buga canjaras

Antonio Rudiger da Lampard Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rudiger ne ya ci wa Chelsea kwallo biyu

Leicester City da Chelsea sun buga canjaras a wasan Premier mako na 25 mai kayatarwa a filin wasa na King Power.

Sakamakon yana nufin har yanzu Leicester ce ta uku da maki takwas tsakaninta da Chelsea, wadda ke ta hudu.

Bayan an buga minti 45 na farko ba tare da wani sakamako ba, wasan ya sauya bayan Antonio Rudiger ya ci wa Chelsea kwallo da ka daga bugun kwanar da Mount ya bugo.

Minti takwas bayan haka Leicester ta farke ta kafar Harvey Barnes, wanda ya buga kwallon kuma ta daki kafar Reece James ta fada raga.

Sai dai Rudiger bai bari an sha su basilla ba, inda ya sake saka wa kwallo kai daga bugun tazarar da Mount ya sake bugowa.

Labarai masu alaka