La Liga: Real Madrid ta doke Atletico a wasan hamayya

Karim Benzema Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Benzema ne ya ci kwallon da ta ba su maki uku rigis

Karim Benzema ne ya yanke hukuncin yadda wasan hamayya na birnin Madrid ya kasance da kwallonsa ta farko da ya taba cin Atletico a filin wasa na Santiago Bernabeu.

Dan wasan kasar Faransa ya zura kwallon ne a minti na 56 daga fasin din da Ferland Mendy ya ba shi bayan Vinicius Jr ya sarrafa kwallon a bangaren hagu.

Atletico wadda ke matsayi na biyar, ba ta ci wasa ba a cikin biyar da ta buga kuma ba ta buga kwallon kirki ba a yau, duk da cewa Angel Correa ya buga kwallon da ta daki tirke.

Real za ta iya cin sama da haka da a ce Jan Oblak bai kare shot biyu da Vinicius ya buga ba.

Wasa na 21 da Real ta buga ke nan ba tare da an doke tawagar Zinedine Zidane din ba kuma ta ci takwas a jere, ciki har da bugun finareti da suka yi da Atletico din a wasan karshe na Spanish Super Cup.

Barcelona da ke mataki na biyu za ta karbi bakuncin Levente ranar Lahadi da karfe 9:00 agogon Najeriya da Nijar.

Labarai masu alaka