Grealish zai bar Villa, Munich ta fasa neman Ronaldo

Aston Villa's Jack Grealish

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasanAston VillaJack Grealish, mai shekara 24, na duba yiwuwar barin kulob din a bazara, duk kuwa da cewa yana son kulob din wanda a can ya soma sana'ar kwallon kafarsa. Manchester United da Manchester City na cikin kungiyoyin da ake sa ran zai zabi komawa. (Telegraph)

Grealish na kallon Manchester United a matsayin inda ya fi son komawa a bazara idan ya bar Aston Villa, ko da yake Barcelona da Real Madridna sha'awar sayensa.(Sun)

A shiryeManchester City suke su amince da shan kaye wajen yunkurin sayen Lionel Messi a kakar wasa mai zuwa bayan da aka gaya musu cewa dan Argentina, mai shekara 32, ba shi da niyyar barin Barcelona. (Express)

Dan wasanManchester City Raheem Sterling ya yi amannar cewa zai koma kan ganiyarsa kafin fafatawar Gasar Zakarun Turai da za su yi da Real Madrid. Kulob din na Spain na sha'awar sayen dan wasan mai shekara 25. (Telegraph)

Tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino yana kila-wa-kala game da zamansa kocin Manchester United a kakar wasa mai zuwa. (Mirror)

Paris St-Germain zasu tura kanakan 'yan wasansu domin kallon yadda dan wasan Ingila Danny Rose, mai shekara 29, ke murza leda a Newcastle bayan daTottenham ta ba da aronsa (Sun)

Za a kyale dan wasanBarcelona dan kasar Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27 - wanda yanzu haka Bayern Munich ta yi aronsa - ya bar kulob din a kan £77m a bazara, inda ake rade-radinManchester United da tsohuwar kungiyar Liverpool suna zawarcinsa. (Express)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Dan wasanManchester City dan kasar Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 28, wanda ake hasashen zai koma Real Madrid ko Barcelona, ya ce "hankalinsa a kwance yake" a kulob din da yake. (Goal)

Roma na fushi saboda Manchester United sun £17m kan tsohon dan wasan Ingila Chris Smalling, mai shekara 30, wanda ke zaman aro a kulob din na kasar Italiya. (Express)

Dan wasan Wales Gareth Bale, mai shekara 30, ya so ya "mayar da kwallon kafar China mai matukar armashi" lokacin da aka yi hasashen cewa zai koma nahiyar Asia a bazarar 2019, in ji jami'insa, ko da yake yanzu yana tunanin ci gaba da zama a Real Madrid kuma ba zai koma Tottenham ba.(Goal)

Dan wasanManchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 22, yana tattaunawa da kamfanin Roc Nation Sports na mawakin na Jay-Z inda zai samu miliyoyin dala. (Mirror)

Bayern Munich sun kawar da yiwuwar sayen dan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo saboda suna ganin dan wasan mai shekara 35 ya tsufa sosai. (Sun)

Ana hasashen cewa tsohon dan wasan Arsenal Aaron Ramsey, mai shekara 29, zai koma Juventus, ganin cewa kwantaragin shekara hudu kawai ya sanya wa hannu a kulob din na kasar Italiya a bara.(Calciomercato - in Italian)

Mai yiwuwaLiverpool su mayar da hanakalinsu wajen sayen dan wasan RB Leipzig Timo Werner, mai shekara 23, a bazara - kuma da alama za su bukaci sayen wani dan wasan na baya. (Athletic, via Team Talk)

Da alamaLiverpool za su bai wa Bournemoutharon dan wasan Wales mai shekara 22, Harry Wilson a bazarar da ke tafe. (Football Insider)

KocinJuventus Maurizio Sarri ka iya neman sayen dan wasan Chelsea,Jorginho, wanda ya taba murza leda a Napoli da Chelsea.(Star)

Barcelonasun gaza a yunkurin da suke yi na sake sayo tsohon kyaftin dinsu Andres Iniesta, mai shekara 35 daga kulob din Vissel Kobena kasar Japan. (Sport)