Makomar Ighalo, Werner, Coutinho, Sancho, Saka, Ramsey da Slimani

Hakkin mallakar hoto Getty Images

An haramta wa dan wasan gabaManchester United Odion Ighalo, mai shekara 30, yin atisaye saboda tsoron cutar coronavirus. (Mirror)

Liverpool na shirin ware fam miliyan £46m domin dauko dan wasan gaba na RB Leipzig Timo Werner, mai shekara 23. (Bild)

Dan wasanBarcelona Philippe Coutinho, mai shekara 27 ya yi watsi da yiyuwar komawa Liverpool inda ya ce yana jin dadi inda yake. (Sun)

Manchester United na sa ido kan matashin dan wasan Arsenal mai shekara 18 Bukayo Saka. (Mail)

KocinEverton Carlo Ancelotti, mai shekara 60, yana tunanin kwantaraginsa a Goodison Park bayan ya sanya hannu kan yarjejeniya mai tsawo a watan Disamba. (Mail)

Real Madrid ta fara sha'awar dan wasan Everton Moise Kean, mai shekara 19. (Teamtalk)

Borussia Dortmund za ta ba dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 19, damar barin kulub din yayin da ta fara neman wasan zai maye gurbinsa. (Telegraph)

Manchester United ake ganin za ta karbo Sancho yayin da Chelsea ke dab da cimma yarjejeniya da Ajax kan dan wasa Hakim Ziyech, mai shekara 26. (Standard)

Liverpool za ta yi hamayya da Real Madrid kan dan wasan tsakiya na Inter Milan Marcelo Brozovic, mai shekara 27. (Star)

Frank Lampard na son cefanen akalla 'yan wasa hudu a wannan bazara inda Chelsea za ta kashe kusan fam miliyan £150. (Metro)

Kocin Juventus Maurizio Sarri ya amince cewa Aaron Ramsey, mai shekara 29, ya kasa dawowa kan ganiyarsa saboda jinyar raunin da ya ji inda ake rade-radin zai koma Ingila tsohuwar kungiyar shi, Arsenal, ko Manchester United koLiverpool ko kumaChelsea da aka ruwaito dukkaninsu na sha'awar dan wasan. (Mirror)

Tsohon kocinJuventus da AC Milan Massimiliano Allegri na jita-jitar cewa zai karbi aikin horar da Manchester United. (Corriere dello Sport, via Mail)

Labarai masu alaka