Salah na cikin tawagar Masar ta gasar Olympic

Mohamed Salah Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Masar ta saka sunan Mohamad Salah cikin 'yan wasa na kwarya-kwarya da za ta je da su Olympic a Tokyo a bana.

Dan wasan mai shekara 27, yana cikin 'yan kwallo 50 da za a fitar da wadan da za su wakilci Masar a fannin kwallon kafa a wasannin.

Za a fara wasannin ne ranar 8 ga watan Agusta a Tokyo, wadda ta yi daidai da ranar fara gasar Premier League kakar 2020/21.

Sai dai kocin Masar, Shawky Gharib ya ce yanke hukuncin wakiltar Masar a Olympic yana hannun Salah da kuma Liverpool da Jurgen Klopp.

Kocin ya kara da cewar ''Ba za muyi wa Salah tilas sai ya buga mana tamaula ba, duk shawarar da ya yanke, idan kuma kungiyarsa ta amince shi za mu bi.''

Wasan kwallon kafa a Olympic na 'yan shekara 23 ne, amma an amince a saka 'yan kwallo uku a kowacce tawaga da suka haura shekarun.

Tun a baya FIFA ta fahimce cewar kungiyoyi ba su da shirin barin 'yan wasa wadan da shekarunsu suka haura su halarci tamaular Olympic.

A cikin watan Yuni ake sa ran kowacce tawaga da ta samu gurbin shiga Olympic za ta mika 'yan wasa 18 da za su buga mata kwallon kafa.

Labarai masu alaka