Olympics: Liverpool na neman karin bayani kan Mohamed Salah - Jurgen Klopp

Salah and Klopp Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce kulob din yana neman karin bayani kafin ya yanke hukuncin barin dan wasan gaba Mohamed Salah ya wakilci Masar a gasar Olympics.

Gasar ta Olympics ta 'yan kasa da shekara 23 ce amma za a bar 'yan wasa uku da suka wuce wadannan shekaru su fafata a gasar.

Salah, mai shekara 27, na cikin jerin 'yan wasan Masar 50 da ake so su fafata a gasar, wacce za a buga wasan karshe ranar takwas ga watan Agusta - wato ranar da za a soma gasar Firimiyar Ingla ta kakar 2020-21.

"Ina son barin dan wasa ya tafi kafin gasar firimiya? Tabas ba na so. Wannan a fili yake," in ji kocin Liverpool Klopp.

"Amma ya kamata mu duba batutuwa da dama. Zan tattauna da Mo a kan wannan batu."

A baya Fifa ta ce ba dole ba ne kungiyoyin gasar firimiya su bar 'yan wasansu da suka girma su halarci gasar wacce za a yi a Tokyo, kuma kocin Masar Shawky Gharib ya ce Liverpool ce za ta yanke hukunci kan ko za ta bar Salah ya je gasar.

Klopp ya ce babu wanda ya tuntubi kulob din game da batun barin Salah ya shiga gasar ta Olympics.

Labarai masu alaka