Tottenham na zawarcin Smalling, Sterling ba zai bar Man City ba

Chris Smalling

Asalin hoton, EPA

Tottenham da Everton na sha'awar sayen dan wasan Manchester United dan kasar Ingila, Chris Smalling, mai shekara 30, wanda a yanzu haka Roma ta yi aronsa. (Corriere dello Sport - in Italian)

Dan wasan Ingila Raheem Sterling, mai shekara 25, zai ci gaba da zama a Manchester City duk da cewa an haramta musu buga gasar Zakarun Turai tsawon shekara biyu, a cewar jami'insa. (Manchester Evening News)

Barcelona na shirin sayo tsohon dan wasan Middlesbrough Martin Braithwaite, mai shekara 28, daga Leganes a wata yarjejeniyar gaggawa. (Mundo Deportivo, via Teeside Gazette)

Kocin Liverpool Jurgen Klopp yana matukar son sayo Timo Werner, ko da yake har yanzu kungiyar bata tuntubi RB Leipzig domin tattaunawa kan dan wasan dan kasar Jamus mai shekara 23 ba. (Independent)

Kocin Lille Christophe Galtier ya ce akwai rashin jituwa tsakanin kungiyar da dan wasanta mai shekara 20, Boubakary Soumare, wanda Manchester United, Liverpool da Chelsea ke zawarcinsa. (Express)

Dan wasan tsakiya na Faransa Matteo Guendouzi, mai shekara 20, yana hankoron ci gaba da zama a Arsenal bayan kungiyar ta cire sunansa daga cikin 'yan wasan da za su fafata a wasan da za su yi da Newcastle ranar Lahadi (Mirror)

An ajiye Guendouzi a benchi bayan cacar bakin da ta faru tsakaninsa da kocin Arsenal Mikel Arteta da jami'an da ke horas da 'yan wasa lokacin da suke atisayen tsakiyar kakar wasa a sansaninsu da ke Dubai. (Goal)

Manchester City ba za ta fuskanci ragin £65m na kayan wasa daga Puma ba ko da kuwa ba a janye haramcin da aka yi wa kungiyar na buga gasar Zakarun Turai ba. (Mail)

Manchester United ta shaida wa Bournemouth cewa sun ba su minti 15 su amince da tayin da suka yi musu na £25m a kan dan wasan Norway Joshua King, mai shekara 28, idan ba haka za su sayar wa China dan wasan. (The Athletic)

Ana sa ran kulob din Brazil Botafogo zai kammala sayen tsohon dan wasan Manchester City Yaya Toure, mai shekara 36, ranar Laraba ko Alhamis. (Globo Esporte - in Portuguese)

Southampton da Burnley na cikin kungiyoyin da ke sha'awar sayo dan wasan Oxford United Rob Dickie, mai shekara 23. (Football Insider)

Ajax na fuskantar rasa 'yan wasa takwas idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa. (The Athletic)