An bai wa dan dambe suna Coronavirus

  • Muhammad Abdu
  • BBC Hausa, Abuja
Bayanan bidiyo,

An bai wa dan damben gargajiya suna Coronavirus

Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyo

An bai wa Abdullahi Ali matashin dan wasan damben gargajiya da ke dambatawa a jihar Kano da ke Najeriya suna ''Coronavirus''.

An haifi Abdullahi a Kurna babban layi da ke karamar hukumar Ungoggo, amma yana zaune a Kunya karamar hukumar Minjibir a jihar Kano.

Abdullahi ya fara wakiltar Kudu, a kuma bara ne sunansa ya kara fita a harkar damben gargajiya.

Hakan ya sa ya fara amsa sunan Autan Dan Alin bata isarka, wani shahararren dan damben Kudu wanda ke kan lokaci.

Autan Dan Ali ya nemi amincewar mahaifiya a wannan sana'ar da yake yi ta kuma amince masa tare da yi masa addu'ar samun nasara.

Matashin dan wasan mai shekara 20, ya gagari sa'anninsa a harkar damben gargajiya, suna jin tsoron yin wasa da shi.

Autan Ali yana daga cikin 'yan damben da ya yi kisa da yawa a filin wasa na Ado Bayero Square a bara.

Bayan Shagon Dan Aliyu da Bahagon Mai Takawasa, sai Autan Dan Ali da ya yi kan-kan-kan da yawan kisa tare da sarkin dambe Garkuwan Cindo.

Kwazon da yake yi ne Sarkin masu shirya wasan damben gargajiya na Najeriya, Mamman Bashar Danliti ya saka masa suna coronavirus.

Danliti shugaban kungiyar damben jihar Kano ya ce dan wasan jarimi ne zai kuma yi fice da suna a damben gargajiya.

Ya kara da cewar Abdullahi na zuwa makaranta da safe, sannan ya je filin dambe da yammaci, sannan ya wuce gida wajen iyaye.

Asalin hoton, Muhammad Abdu

Haka ma a lokacin da cutar Ebola ta addabi duniya, an bai wa Abdulrazak sunan cutar, dan damben Kudu wanda ya yi fice a wasan.