An bai wa Barcelona damar daukar dan kwallo

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Mahukuntan gasar La Liga sun bai wa Barcelona dama ta musamman da su sayo 'yan kwallo, bayan da aka rufe kasuwa.

Hakan ya biyo bayan da dan wasan Barcelona da Faransa, Ousmane Dembele ya ji raunin da zai yi jinyar wata shida.

Cikin dokar La Liga, kungiya za ta iya neman izinin sayen dan wasa, idan wanda take da shi ya yi raunin da zai yi jinyar sama da wata biyar.

Kuma dan kwallon da za ta dauka ya zama wanda bai da yarjejeniyar da wata kungiyar amma mai wasa a Spaniya, kuma ba zai buga gasar Zakarun Turai ba.

Dan wasan tawagar Uruguay, Luis Suarez na jinyar wata hudu tun daga watan Janairu, sai Dembele da ya ji rauni a watan Fabrairu a lokacin atisaye.

Barcelona ce ta mika wa La Liga takardun shaidar jinyar da Dembele zai yi, bayan da hukumar ta yi nazari ta kuma amince da bukatar kungiyar ta Camp Nou.

Dembele na fama da jinya tun komawarsa Barcelona daga Dortmund a 2017, kuma wasa uku ya buga a kakar bana.

Barcelona tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki daya tsakaninta da Real Madrid wadda take ta daya.