Manchester United ta ziyarci Stamford Bridge

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan mako na 26 a gasar cin kofin Premier ranar Litinin.

Bayan da United ta yi atisaye a Spaniya a dan karamin hutun da ta yi, kungiyar za ta kara sa kwazo don neman gurbin Champions Legaue na badi.

Chelsea wadda take ta hudu a teburi ta bai wa United tazarar maki shida, ita kungiyar ta Old Trafford tana ta tara a teburin.

Ole Gunnar a matsayin kocin United ya samu nasara a kan Chelsea a wasa ba a doke shi ba, ya kuma yi nasara a fafatawa biyu a Stamford Bridge.

A cikin watan Agusta ne United ta doke Chelsea 4-0 a gasar Premier a Old Trafford.