Barca ta musanta hayar kamfani don caccakar Messi

barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar Barcelona ta musanta zargin da ake cewar ta yi hayar kamfanin da zai dunga caccakar Lionel Messi da Gerard Pigue.

Wani gidan radiyo ya ce Barcelona na son kare martabar shugaba Josep Maria Bartomeu da kimarsa daga wadan da ba su amince da shi ba.

SER Catalunya ya ce Barca na aiki da wani kamfani wanda zai samar da ra'ayoyi a kafar sada zumunta domin cimma buri.

Sai dai Barcelona ta musanta zargin yin alaka da wasu masu shafukan sada zumuntar.

Kungiyar ta Camp Nou ''Ta bukaci tantance labarin da aka yada, za kuma ta dauki matakin shari'a da duk wadan da suka ci gaba da yada batun'' in ji wani jawabi da ta fitar.

Kamar yadda SER Catalunya ta ce wasu kafar kasuwanci su 13 na kula da shafukan mutane da yawa a Twitter da facebook.

Ta kara da cewar an caccaki shafukan Messi da Pique da Pep Guardiola da tsoffin 'yan wasa kamar Xavi da Carles Puyol da wasu da ke hamayya da Bartomeu.

Barcelon ta mayar da martani cewar kafar kasuwanci su 13 masu kula mata da gyare-gyare ko tsarin kafar sada zumuntar ta ne, amma babu abinda ya hada su da shafukanta.