Watakila Son ya gama buga kwallo a kakar bana

Tottenham

Asalin hoton, Getty Images

Jose Mourinho ya ce baya tsammani Son Heung-min zai kara buga wa Tottenham kwallo a bana, sakamakon raunin da ya ji.

Dan wasan tawagar Koriya ta Kusu, mai shekara 27, ya yi rauni ne a wasan da Tottenham ta doke Aston Villa da ci 3-2 ranar Lahadi a gasar Premier.

Ana sa ran a cikin makon nan za a yi wa Heung-min aiki, bisa karayar da ya yi a hannunsa, a fafatawar da ya ci kwallo biyu.

Tun a ranar Talata Tottenham ta fitar da sanarwa cewar Son zai yi jinyar makonni ne.

Tottenham ta rubuta sako cewar za ta yi rashin dan kwallon, sai dai Mourinho ya ce da shi ne mai rubutun ba haka zai aike da sakon ba.

Kawo yanzu Mourinho yana da zabin amfani da Lucas Moura ko Steven Bergwijn da ta dauka a Janairu ko kuma Troy Parrott.