'Yan PSG da za su kara da Dortmund a Champions League

PSG

Asalin hoton, Getty Images

Paris St Germain za ta ziyarci Borrusia Dortmund domin buga wasan zagaye na biyu a gasar Champions League ranar Talata.

PSG ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta ja ragamar rukunin farko da maki 16, ita kuwa Dortmund ita ta yi ta biyu a rukuni na shida da maki 10.

Wannan ne wasa na uku da kungiyoyin za su kara a gasar Turai, inda suka tashi 1-1 a 2010 a Jamus da 0-0 a Faransa.

Haka kuma Dortmund da PSG sun fafata a wasan sada zumunta karo biyu, ind PSG ta ci 2-1 a Jamus a 1990 da kuma 3-1 a Paris a 1992.

Mai jan ragamar PSG, Thomas Tuchel ya kuma taba horas da Borrusia Dortmund.

'Yan wasa biyu sun buga wa kungiyoyin kwallo da ya hada da Christian Wörns da kuma Abdou Diallo, sai dai Dan Axel Zagadou bai yi wa PSG babban wasa ba.

Paris Saint-Germain za ta buga wasa na 111 a Champions League, inda ta yi nasara a karawa 60 da canjaras 22 aka doke ta sau 28.

Wannan kuma shi ne karawa ta 223 a gasar Zakarun Turai da PSG za ta buga, inda ta ci wasa 116 da canjaras 52 da rashin nasara a wasa54.

'Yan wasan PSG da aka je da su Dortmund:

 • BERNAT Juan
 • BULKA Marcin
 • CAVANI Edinson
 • DI MARIA Angel
 • DRAXLER Julian
 • GUEYE Idrissa
 • HERRERA Ander
 • ICARDI Mauro
 • KEHRER Thilo
 • KIMPEMBE Presnel
 • KOUASSI Tanguy
 • KURZAWA Layvin
 • MARQUINHOS
 • MBAPPÉ Kylian
 • MEUNIER Thomas
 • NAVAS Keylor
 • NEYMAR JR
 • RICO Sergio
 • SARABIA Pablo
 • THIAGO SILVA
 • VERRATTI Marco

Wadan da ke yuin jinya:

 • AOUCHICHE Adil
 • BAKKER Mitchel
 • CHOUPO-MOTING Eric Maxim
 • DAGBA Colin
 • DIALLO Abdou
 • INNOCENT Garissone
 • MBE SOH Loïc
 • PAREDES Leandro