Mai kuke son sani game da wasan Atletico da Liverpool?

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta ziyarci Atletico Madrid a wasan zagaye na biyu a gasar Champions League da za su fafata ranar Talata a Wanda Metropolitano.

Wannan ne karo na hudu da kungiyoyin za su kece raini a gasar UEFA, bayan da suka yi canjaras biyu, kowanne ya ci wasa daya.

Atletico ta doke kungiyar Ingila sau 11 da canjaras 12 da rashin nasara a wasa shida, sannan ta ci kwallo 39 aka zura mata 33 a raga.

Karawar da Atletico ta ci kwallo da yawa shi ne 3-0 da ta yi nasara a kan Manchester United a UEFA Cup Winners ranar 23 ga watan Oktobar 1991.

Da kuma cin Chelsea 4-1 a UEFA Super Cup ranar 31 ga watan Agustan 2012.

Kungiyoyin biyu suna daga cikin wadan da ke sawun gaba a kai hare-hare, inda Liverpool tana ta hudu, Atletico ce ta shida.

Haka kuma Liverpool mai rike da kofi ce ta biyu wajen raga kwallo a gasar zakarun Turai, bayan Manchester City.

'Yan kwallon da ake sa ran za su buga wa kungiyoyinsu karawar.

'Yan wasan Atletico Madrid:

Masu tsaron raga: ADAN da OBLAK

Masu tsaron baya: J.M. GIMÉNEZ da ARIAS da LODI da SAVIC da FELIPE da HERMOSO da VRSALJKO

Masu wasan tsakiya: THOMAS da KOKE da SAUL da LEMAR da MARCOS LLORENTE da VITOLO da kuma CARRASCO.

Masu buga gaba: MORATA da CORREA da kuma DIEGO COSTA.

'Yan wasan Liverpool:

Masu tsaron raga: ALISSON da ADRIAN da kuma KELLEHER.

Masu tsaron baya: VAN DIJK da LOVREN da GOMEZ da ROBERTSON da MATIP da kuma ALEXANDER-ARNOLD.

Masu buga tsakiya: FABINHO da WIJNALDUM da MILNER da KEITA da HENDERSON da OXLADE-CHAMBERLAIN da kuma LALLANA.

Mau buga gaba: FIRMINO da MANE da SALAH da MINAMINO da kuma ORIGI.