Liverpool ta samu gurbin Chamapions League na badi

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta zama kungiyar farko da ta samu gurbin shiga gasar Champions League na kakar 2020/2021.

Cin Chelsea da Manchester United ta yi ne ya tabbatar da cewar Liverpool za ta kare gasar Premier cikin hudun farko komai runtsi.

Liverpool wadda take ta daya ta bai wa Tottenham ta biyar tazarar maki 36 a teburi, kuma sauran wasa 12 a karkare gasar Premier bana.

Asalin hoton, BBC Sport

Tottenham za ta buga da Chelsea a karshen mako, hakan na nufin koda Jose Mourinho zai lashe sauran wasansa, ita kuwa Liverpool ta yi rashin nasara a dukkan karawar da ta rage, duk da haka Chelsea za ta kare da maki 74 a kasan Liverpool.

Karo biyu Liverpool wadda ke rike da kofi na kai wa champions League, za kuma ta kara da Atletico Madrid a wasan zagaye na biyu ranar Talata.

Liverpool ita ta farko tsakanin kungiyoyin Turai da ta kai gasar Zakarun nahiyar da za a yi a 2020/2021.

Da yake hukumar nahiyar Turai ta yanke hukuncin dakatar da Manchester City, hakan na nufin duk kungiyar da ta yi ta biyar a Premier za ta je Champions League a badi.

Kididdiga ta nuna cewar Liverpool za ta lashe Premier bana a wasan da za ta buga da Bournemouth ranar 7 ga watan Maris.

A lokacin ana sa ran Liverpool ta ci dukkan wasanninta, sannan Manchester City da Leicester City su yi tuntube a wasannin da suka rage.

Manchester United ce keda tarihin lashe kofin Premier da wuri karkashin jagorancin Sir Alex Ferguson a kakar 2000/01 ranar 14 ga watan Afirilu.